TSK

TSK · Ayyukan Manzanni 21:13

مراجع Treasury of Scripture Knowledge في Litafi Mai-tsarki.

العودة إلى المقطع

Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa.

Ko da ana tsiyaye ni kamar sadaka a kan hadaya da kuma hidimar bangaskiyarku, na yi farin ciki, kuma na yi farin ciki tare da ku duka.

Yanzu ina murna da wahala ta domin ku. A jikina cika abin da ya rage cikin wahalar Almasihu domin jikinsa wadda itace ikilisiya.

Ba bu sojan da zai yi bauta yayin da ya nannade kansa da al'amuran wannan rayuwar, domin ya gamshi shugabansa.

Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani.

Suka ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu, gama ba su kaunaci ransu ba, har ga mutuwa.