Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, ''Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?
TSK
TSK · Markus 7:21
Treasury of Scripture Knowledge references in Litafi Mai-tsarki.
Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta.
Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa.”
Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa.
Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya.
Domin a da, mu da kan mu marasa tunani ne kuma masu rashin biyayya. Mun kauce hanya muka zama bayi ga sha'awoyin duniya da annashuwa. Mun yi zama a cikin mugunta da kishi. Mu lalatattu ne kuma muna kiyyaya da junanmu.
Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba?
Wannan mutum kuma baya kara zaman biye wa muguwar sha'awar mutumtaka, amma sai dai nufin Allah dukkan sauran kwanakinsa a duniya.