Yesu ya ga Natana'ilu yana zuwa wurinsa sai yayi magana game da shi, “Duba, Ba-Isra'ile na hakika wanda babu yaudara a cikinsa.”
TSK
TSK · Yohanna 3:21
مراجع Treasury of Scripture Knowledge في Litafi Mai-tsarki.
Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada 'ya'ya shi kadai sai ya zauna cikin itacen, haka kuma ba za ku iya ba, sai kun zauna ciki na.
Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni.
Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya,
Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya.
Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi.
ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin.
Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani.
Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa.
Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
¶ “Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Sardisu rubuta: ' Wadannan ne kalmomin wanda yake rike da ruhohi bakwai na Allah da taurari bakwai. “Na san abin da ka aikata. Ka yi suna cewa kana raye amma kai mattacce ne.