Ikrarin Bangaskiyar Orthodox

The Orthodox Creed

Hakika mun gaskata da Allah ɗaya, Allah Uba, Mai iko duka, Mahaliccin sama da ƙasa da dukan abubuwan da ake gani da waɗanda ba a gani ba.

Mun gaskata da Ubangiji ɗaya Yesu Almasihu, makaɗaicin Ɗan Allah, haifaffe daga wurin Uba kafin dukan zamani. Haske daga Haske, Allah na gaskiya daga Allah na gaskiya; haifaffe, ba halitta ba; mai zatin ɗaya da Uba; ta wurinsa aka yi kome.

Domin mu mutane da domin cetonmu ya sauko daga sama; ya ɗauki jiki ta wurin Ruhu Mai Tsarki da Budurwa Maryamu, ya zama mutum.

An gicciye shi dominmu a zamanin Buntus Bilatus, ya sha wuya aka binne shi; a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu bisa ga Nassosi.

Ya hau zuwa sama, yana zaune a hannun dama na Ubansa; zai sāke zuwa cikin ɗaukaka domin ya yi wa masu rai da matattu shari'a; mulkinsa ba zai ƙare ba.

I, mun gaskata da Ruhu Mai Tsarki, Ubangiji Mai ba da rai, wanda yake fitowa daga wurin Uba; ana masa sujada da ɗaukaka tare da Uba da Ɗa; wanda ya yi magana ta bakin annabawa.

Da kuma Ikilisiya ɗaya, mai tsarki, ta duniya duka, ta manzanni. Mun shaida baftisma ɗaya domin gafarar zunubai.

Muna jiran tashin matattu da rai na zamani mai zuwa. Amin.