Story
Mai Tsarki Abanoub Yaron Shahidi Abanoub bai wuce shekara goma sha biyu a duniya ba sa'ad da ya sami rawanin shahada a hannun gwamnan Romawa. A rana ta talatin da daya ga watan Yuli ce Cocinmu ke yin bikin rasuwarsa, a matsayin ranar haihuwarsa cikin rai madawwami.
Har yau ana ajiye gawar Mai Tsarki Abanoub, tare da gawarwakin Kiristoci da yawa da suka yi shahada tare da shi, a cikin cocin Budurwa Mai Tsarki Maryamu da Mai Tsarki Abanoub a birnin Samanoud. Ana kuma cewa Iyalin Mai Tsarki sun ziyarci wannan wuri a lokacin tafiyarsu zuwa kasar Masar. Cocin har yanzu tana riƙe da rijiyar da Ubangiji Yesu da Mai Tsarki Maryamu da Mai Tsarki Yusufu suka sha daga gare ta. Har wa yau ana ci gaba da ganin bayyanuwa da ababen al'ajabi masu yawa a cikin wannan coci. An haifi Abanoub a wani gari mai suna Nehisa a yankin Delta na Kogin Nilu, kuma shi ne ɗa tilo na iyaye Kiristoci masu tsoron Allah waɗanda suka rasu tun yana ƙarami. Sa'ad da ya kai shekara goma sha biyu, ya shiga cikin coci ya ji firist yana gargaɗin jama'a su tsaya a ƙarƙashin bangaskiya cikin tsanantawar da Diocletian, Sarkin Romawa, ya tā da.
Abanoub ya karɓi Sirrai Masu Tsarki, sa'an nan ya yi addu'a ga Allah ya bishe shi zuwa wurin da zai iya shaida bangaskiyarsa ga Yesu Ubangijinmu. Bayan haka Abanoub ya fita, ya raba dukan abin da yake da shi ga matalauta. Sa'an nan ya kama hanya da ƙafa zuwa wani birni mai suna Samanoud. Yayinda yake tafiya, sai ya ga Mala'ika Sarki Mika'ilu cikin ɗaukaka ta samaniya. Ganin ya yi girma har Abanoub ya faɗi ƙasa, amma Mala'ikan Sarki ya ɗaga shi, ya gaya masa cewa dole ne ya sha wahala kwana uku a Samanoud kuma zai shaida wa Yesu Kiristi a waɗansu wurare kuma.
Da isowarsa Samanoud, Abanoub ya je wurin gwamnan Romawa ya bayyana bangaskiyarsa a fili. Ya kuma zagi gumakan gwamnan. Gwamnan ya yi fushi sosai, ya umarta a yi masa bulala a cikinsa. Sojoji suka doke Abanoub da ƙarfi har hanjinsa ya zubo daga cikinsa. Amma Mala'ikan Sarki Mika'ilu ya warkar da shi ta hanyar al'ajabi. Sa'an nan gwamnan ya saka shi a kurkuku tare da waɗansu Kiristoci waɗanda kasancewarsa a tsakaninsu ya ƙarfafa su, daga baya kuma suka yi shahada saboda sunan Yesu.
Washegari, gwamnan ya kai Abanoub a kan jirgin ruwa zuwa wani birni mai suna Atrib, kuma a matsayin hukunci, ya rataye Abanoub a juye daga jirgin jirgin ruwan. Sojojin, tare da gwamnansu, suka fara shan giya da rawa da bugun Abanoub a baki. Hanci na Abanoub ya yi zub da jini, amma ba zato ba tsammani, sojojin suka makance gwamnan kuma ya zama shanyayye. Cikin azabarsu suka yi masa kuka suka ce, "Muna roƙonka Abanoub, ka yi addu'a ga Allahnka ya warkar da mu. Gama in an warkar da mu, za mu zama Kiristoci."
Mai Tsarki Abanoub ya amsa, "Wannan zai faru ne kawai a Atrib, domin kowa a can ya san cewa babu wani Allah sai Kiristi." Sa'ad da suka isa Atrib, dukansu suka warke, suka yi kuka da farin ciki suka ce, "Mu Kiristoci ne! Mun gaskata da Allahn Abanoub." Sa'an nan suka tuɓe rigunan soja suka jefar da su a ƙasa a gaban gwamnan Atrib. Sai gwamnan ya yi fushi sosai, ya umarta a kashe su.
A Atrib, an azabtar da Abanoub ƙwarai, wani lokaci ta hanyar bulala wani lokaci kuma ta hanyar ɗaure shi a kan gadon ƙarfe a ƙuna wuta a ƙarƙashinsa. Amma a cikin dukan waɗannan tsananin, Ubangiji ya bayyana ikonsa kuma aka ceci Abanoub. Sakamakon waɗannan ababen al'ajabi, masu kallo da yawa suka zama Kiristoci, suka kuma sami rawanin shahada. Sa'an nan gwamnan ya umarta a yanke hannaye da ƙafafun Abanoub. Ba zato ba tsammani, Mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama, ya mayar da hannaye da ƙafafu a wura(nsu), ya warkar da shi. Sa'an nan Abanoub ya tashi ya yi tafiya a gaban kowa. Ɗaruruwan mutane suka zama Kiristoci sakamakon wannan al'ajabi.
Cikin takaici, gwamnan ya kira waɗansu daga cikin gwanayen masu sihiri a ƙasar, ya nemi su taimaka masa ya kayar da Abanoub. Suka ba da shawara cewa a jefa shi ga macizai masu dafi. "Waɗannan macizai suna da isasshen dafin da zai kashe mutum ɗari biyu ko uku," in ji su. Saboda haka suka saka Abanoub a cikin ɗaki tare da macizan, amma Allah, wanda ya rufe bakunan zakoki a zamanin Daniyel, ya hori macizan kuma ba su cuci Abanoub ba. Da safe, ga mamakin kowa, Mai Tsarki Abanoub ya fito daga ɗakin da rai.
Sa'an nan ba zato ba tsammani ɗaya daga cikin macizan ya rarrafe ya fito daga ɗakin ya naɗe kansa kewaye da wuyan gwamnan. Mutumin ya fara rawan jiki ya yi kuka ya ce, "Da sunan Yesu Allahnka, ka yi mini jinƙai kada ka bar maciji ya cuce ni." Sai Mai Tsarki, wanda yake ƙaunar kowa - aboki ko maƙiyi - kamar yadda Linjila ta umarta, ya yi addu'a daga zuciya, sa'an nan ya umarci maciji ya sauka kada kuma ya cuci gwamnan. A wannan rana, mutane da yawa da suke a wurin har da masu sihiri uku suka gaskata da Yesu.
A ƙarshe ɗaya daga cikin mashawartan gwamnan ya gaya masa ya fille kan Mai Tsarki ya kawo ƙarshen wannan al'amari. Saboda haka gwamnan ya umarci sojoji su kashe Mai Tsarki Abanoub da takobi. Wani mutum mai bangaskiya mai suna Mai Tsarki Yuliyus ya naɗe gawar Abanoub cikin lallausan tufar lilin ya aika da shi zuwa garinsu Nehisa inda aka binne shi.
A shekara ta 960 bayan Haihuwar Almasihu, an mai da jikinsa zuwa cocin Budurwa Mai Tsarki Maryamu a Samanoud inda yake kwance har yau. A tsawon shekaru, Abanoub ya yi bayyanuwa da yawa a wannan coci. Yakan bayyana a matsayin yaro ɗan shekara goma sha biyu yana wasa da yara masu shekarunsa. Wani lokaci ya shiga tsakani a faɗa tsakanin waɗansu yara Kiristoci da Musulmi. Wannan al'amari ya tā da fushin ɗaya daga cikin manyan Musulmi da suke zaune kusa da cocin. Firist na cocin, wanda tsoho ne, ya yi fushi sa'ad da ya sami labarin abin da ya faru. Cikin fushinsa ya hana Yaron Mai Tsarki bayyana. Abin mamaki, Mai Tsarki ya yi biyayya ga shawarar firist kuma bayyanuwar ta tsaya shekaru da yawa.
A shekara ta 1974 ne kawai, sa'ad da aka naɗa Mahaifi Abanoub Louis firist a wannan coci, ya kira biskofai biyu waɗanda suka zo cocin kuma bayan sun yi addu'a da himma, suka yardar wa Mai Tsarki ya bayyana in ya so. Kusan a cikin makonni biyu aka shaida bayyanuwa ta farko, sa'an nan kuma ababen al'ajabi da bayyanuwa masu yawa suka biyo baya.
Wani sanannen biskof ya ziyarci Montreal kwanan nan ya yi magana game da ababen al'ajabi da shi kansa ya gani. Ya ce, "Wata rana, ina ziyarar Samanoud, na halarci yin Mass a cocin Budurwa Mai Tsarki Maryamu da Mai Tsarki Abanoub. Mass ɗin yana tsakiyar mako, kuma mutane kaɗan ne suka halarta. Bayan mun gama, na yi nuni game da yadda wannan coci take da kyau, da kuma yadda na ji daɗin yin Mass a cikinta, sai dai wani ƙaramin abu ɗaya." Na ƙara da cewa a tsawon addu'o'in wani ƙaramin yaro ya yi ta shigowa da fitowa daga ƙofar gaba. Firist ya gaya mini cewa bai ga wani ƙaramin yaro ba, kuma manya kaɗan ne suka halarci Mass ɗin. Sai ya yanke shawarar cewa wannan ƙaramin yaro Mai Tsarki Abanoub ne.
Wani mutum kuma ya ce bayan ya halarci Mass, ya kama hanya yana riƙe da jakar takardu. "Ana ruwan sama, sai na zame na faɗa cikin tafki na ruwa. Sai wani ƙaramin yaro ya zo gudu a wajena, ya taimake ni na tashi tsaye. Ya ba ni jakar takarduna, ya gaya mini in haye zuwa ɗayan gefen titin. Na yi mamaki da na gane cewa tufafina da jakar takarduna sun bushe ƙaƙaf. Sa'an nan na nemi ƙaramin yaron, amma ya ɓace."
Bari albarka da addu'o'i da roƙe-roƙe na wannan babban Shahidi, Yaron Mai Tsarki Abanoub, su kasance tare da mu. Amin.